Yadda Za Ka Tura SmartChain Na $1 Zuwa Truswallet Daga Wata Exchange

Yadda Za Ka Tura SmartChain Na $1 Zuwa Truswallet Daga Wata Exchange

Mutane da dama suna qorafin cewa a yanzu ba sa iya Tura Smart Chain na qasa da $5 daga Binance zuwa Truswallet,

Wannan haka yake, kuma ya samo asaline ta dalilin tashin da BNB yayi daga $300 zuwa har $640+,

Wannan shine abin da yake faruwa duk lokacin da BNB ya tashi mafi qarancin abin da zaka iya withdraw  na BNB daga Binance zuwa wata exchange yana qaru wato “Minimum Withdrawal”

Haka idan ya sauko, Minimum withdrawal yana saukowa, 

A yanzu mafi qarancin abin da za ka iya cirewa na BNB daga Binance zuwa wata exchange shine 0.02BNB wanda yana daidai da kusan $12,

A yanzu zamuyi bayanin Hanyoyi guda 2 da ake iya Tura Smart Chain na $5 zuwa qasa ko da $1 ce zuwa Truswallet 


Ga Hanyoyin:-

1. Hanya ta farko shine ta hanyar yin amfani da da kasuwar HOTBIT wato HOTBIT EXCHANGE,

Domin a yanzu a kasuwar HOTBIT basu da wani mafi qarancin Smart Chain da zaka iya turawa zuwa wata kasuwar,

Wanda hakan yake nufin ko na $1 kana iya turawa zuwa wata EXCHANGE, 

Sai dai ka lura za ka tura ne ta hanyar BEP20 ba BEP2 ba,

Saboda BEP2 yana da Minimum withdrawal na 0.01BNB wanda yakai na kusan $6,

Saboda haka zakayi amfani da BEP20 ne, 

Sannan Gas fee din da za a dauka shine na 0.001BNB kusan $0.6 kenan.


2. Hanya ta biyu itace ta hanyar tura BUSD daga Binance zuwa Trustwallet, sai kayi swapping dinta ta koma Smart Chain kamar yadda kake Swapping na sauran coins, 

BUSD farashinsu daya da USDT, 

Idan USDT gareka sai ka shiga Market ka yi searching na BUSD sai ka sayeta da USDT sannan sai ka turata zuwa Truswallet sai kuma kayi swapping dinta ta koma SmartChain, 

A yanzu tura BUSD daga Binance zuwa kowacce Exchange kyauta ne babu Gas Fee ko kadan.

Sai dai dole ka tanadi Smart Chain wanda za a dauka a matsayin GAS FEE lokacin da zakayi swapping din BUSD ta koma Smart Chain. 

Wadannan sune hanyoyi mafi sauqi da za ka iya tura Smart chain  na qasa $5 zuwa Truswallet.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button