Yadda Za Ka Yi Maganin Masu Kutse (Hackers) A WHATSAPP Ta Hanyar Saka Two-Step Verification

Yadda Za Ka Yi Maganin  Masu Kutse (Hackers) A WHATSAPP Ta Hanyar Saka Two-Step Verification


Kamar yadda sanin duk wani mai amfani da kafafen sada zumunta na zamani ne a yanzu ba ka fi qarfin a maka kutse cikin Account a qwace maka shi ba,

Duk wani kafafen sada zumunci a yanzu masu kutse  a yanzu suna iya kutsawa cikinsa su qwaceshi cikin sauqi, 

A yanzu kusan kafar sada zumunta ta Facebook Account itace wadda aka fi kutse ana sacewa mutane Account dinsu, 

Idan an sace sai ka ga ana amfani da Account din wajen neman taimakon kudi ko katin waya ko kuma ayi amfani da shi wajen yada abubuwan da basu dace ba kamar hotunan batsa da makamantansu, 

Da yawa wannan kutsen yana faruwa ne ta dalilin sakacin wanda aka yiwa kutsen, 

Akwai dalilai wanda suke zama sababin qwace Account din mutane a kafafen sada zumunta na zamani, 

Daga cikin dalilan akwai yin amfani da rarraunan password (weak password) a maimakon amfani da qaqqarfan Password (Strong Password) sai ka ga mutum yana amfani da lambar waya ko wasu lambobi masu sauqin ganewa a matsayin password, InshaAllahu A rubutunmu na gaba za mu zo da bayani akan Wanne irin Password ya kamata kana amfani da shi, 

Sannan daga cikin wasu dalilan akwai yawan shiga Links wanda suke cewa suna bayar da free data ko recharge card ko kudi da sauransu, suma duk hanyoyine da ake bi wajen yin dabara don sace account din kafafen sada zumunta na zamani,

Daga cikin matakan da ake bi don bada kariya ga Account na sada zumuta shine amfani da Two-Step Verification, 

Shi Two-Step Verification wata hanya ce ta qarfafa tsaro a Account na kafafen sada zumunta, 

Matuqar kana amfani da shi to ina tabbatar maka kafi qarfin a maka kutse ko a qwace maka Account dinka na kafafen sada zumunta, 

SHIGA NAN Ka karanta Yadda Za Ka Zama P2P-BOSS Kafin Qarfin Damfara A P2P 

A yau shafin www.nasara.com.ng zai yi bayani akan yadda za ka saka Two-Step Verification a WHATSAPP, 

Domin a yanzu tabbas ana yiwa mutane kutse a whatsapp ba tare da sun sani ba, ana amfani da Account dinsu na whatsapp ana tura wasu saqonni zuwa ga đaiđaikun mutane ko kuma Groups, 

Sai ka ga an tura wani saqo wanda shi mai ainishin Account din bai san anyi amfani da Account dinsa an tura saqon ba, sai dai idan an ankarar da shi, 

Amma matuqar ka saka Two-Step Verification ka tsira daga sharrin ‘Yan DanDatsa wato hackers kenan.


Yadda Za Ka Saka Two-Step Verification  A WHATSAPP

1. Bayan ka shiga cikin whatsapp Za ka wasu Digo a jere guda uku da suke sama a sukurwar dama, sai ka ta6asu.

2. Sai ka shiga SETTINGS za ka ganshi shine a qasa.

3. Sai ka shiga ACCOUNT 

4. Sai ka shiga TWO-STEP VERIFICATION.

5. Bayan ka shiga Two-step verification zai sanar da kai cewa shi Two-step verification qarin tsaro ne wanda a duk lokacin da zakayi LOGIN cikin whatsapp zai buqaci ka shigar da lambobin tsaro wato “Pin Number”, Hakan yana nufin bayan verification code da ake turo maka ta lamabar wayarka lokacin da zakayi Login whatsapp to akwai kuma qarin Pin number da za a buqaci ka shigar wadda itace kake qoqarin sakawa wato Two-step verification. 

6. Bayan ka aminta da wannan bayanai na su sai ka danna ENABLE domin saita Pin number, 

7. Bayan ka danna ENABLE zai kai ka shafi na gaba wanda anan ne za ka za6i lambobin tsaro na sirri wato Pin number guda shida sai ka shigar, Shafin www.nasara.com.ng yana fatan zaka za6i lambobi masu wahalar ganewa ga waninka amma masu sauqin tunawa agareka. 

8. Bayan ka shigar da lambobin tsaro guda shida, Za ka ganka a shafi na gaba wanda anan ne za ka qara maimaita lambobin tsaron guda shida a matsayin matakin tabbatarwa wato “CONFIRMATION“.

9. Mataki na ga a shafi na gaba shine za su buqaci ka shigar da adireshinka na Email, wanda da shi ne zakayi amfani wajen dawo da account dinka na whatsapp bayan ya samu matsala ko ka manta Pin dinka.

SHIGA NAN Ka Karanta Yadda Ake ABITRAGE Tsakanin Kasuwanni Biyu

10. Akwai wajen da aka rubuta SKIP ma’ana wai kawai a wuce wannan matakin ba sai ka saka adireshin Email ba, To ko ka ta6a domin wucewa ba zai wuce ba, zai sanar da kai cewa idan ka manta lambobin tsaronka wato pin number to ba zaka iya sake yin rijista da whatsapp ba, hakan yana nufin dole ka shigar da adireshinka na email.

11. Shima shigar da adireshin email matakai ne guda biyu,  za ka saka sannan za ka qara sakawa a matakin tabbatarwa wato “Confirmation“.

12. Bayan ka shigar da adireshin email shikenan ka gama saka Two-step verification a whatsapp dinka. 

13. Yana da kyau ka sani duk lokacin da za ka yi Login cikin account dinka na whatsapp zai buqaci ka shigar da lambobin tsaro na sirri guda shiga da ka za6a lokacin kunna Two-step verification.

14. Haka lokaci zuwa lokaci ba sai zakayi Login ba haka idan ka zo shiga cikin whatsapp zai buqaci ka shigar masa da lambobin tsaron guda shida, ba don komai ba sai don bada kariya ga whatsapp dinka.

15. Idan ka ga dama kana iya zuwa ka cire Two-step verification wato kayi “DISABLE” dinsa, 

16. Haka kana iya canja lambobin tsaro wato “CHANGE PIN”

17. Sannan kana iya canja adireshin email wato “CHANGE EMAIL ADDRESS”.

18. Duka uku nan zakayi hakan ne ta hanyar bin hanyar da mukayi bayani yadda za ka saka Two-step verification. 

19. Za ka ta6a Dot guda uku, sai ka shiga setting, sai ka shiga Account, sai kuma Two-step verification duk za ka gansu anan. 

20. Kar ka manta wannan tsaro yana da muhimmanci ga kai kanka da kuma mutanen da kake mu’amala da su a whatsapp, Rashin daukan matakin saka Two-step verification zai iya zama illa agareka da mutanen da kake mu’amala da su a kafar sadarwa ta whatsapp, Allah ya Kiyaye.

SHIGA NAN Ka Karanta Yadda Za Ka Qara Girman Memory Din Wayarka

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button