Yadda Za Ka Yi Siyayya Kamar A Market Price Cikin HOTBIT

Yadda Za Ka Yi Siyayya Kamar A Market Price Cikin HOTBIT 


Market Price ko kuma farashin kasuwa shine ainishin farashin coin ko token a  lokacin da kake son siya ko siyarwa,

Kamar yadda mu ka sani kana iya siyan  token ko coin a farashin kasuwa  nan take wato Market Price ko kuma ka daidata a siya maka idan ya sauko qasa da farashin kasuwa wato Buy Limit Order,

Haka ana iya siyar da coin ko token a ainishin farashin kasuwa nan take wato Market Price ko kuma ka daidaita shi a siyar maka da shi lokacin da ya tashi sama da farashin kasuwa wato Sell Limit Order. 

Cikin kasuwanni na Crypto Currency akwai kasuwannin da suke da Market Price da Limit Order sannan akwai wanda suke da iya Limit Order, 

Yawancin manyan kasuwanni na Crypto Currency kamar BINANCE, KUCOIN da OKEX duk suna da market price Order da Limit Order,

Amma akwai kasuwannin da basu da Market Price sai Limit Order kadai daga ciki akwai HOTBIT, 

Rashin Market Price Order a kasuwar HOTBIT yana ba da wahala wajen siye da siyarwa, 

Wanda siya ko siyarwar da za kayi shi cikin lokaci qanqani amma a kasuwar HOTBIT sai ya daukeka dogon lokaci, 

Hakan ne ya sa shafin www.nasara.com.ng muka ga ya dace yayi bayanin yadda ya kamata a yi siyayya a kasuwar HOTBIT cikin sauqi kamar a market price.

SHIGA NAN  Ka Karanta Yadda Za Ka Magance Matsalar Volume Of Order Placement Must Be The Integral Multiple Of 1000000

Yadda Za Ka Yi Siyayya A Kasuwar HOTBIT Cikin Sauqi Kamar A Market Price

Duk da babu market price a kasuwar HOTBIT, amma shafin www.nasara.com.ng yau ya kawo muku yadda za kuyi siyayya ko ku siyar a kasuwar HOTBIT nan take kamar a market price din.

Yadda zakayi shine:-

Bayan ka je kan coin ko token da kake son siya ko siyarwa, Bayan ka shiga BUY idan siya zakayi  kenan, ko kuma SELL idan siyarwa zakayi, 

Sai ka duba daga Gefen dama akwai wasu lambobi a jere wasu da koren rubutu wasu da jan rubutu, sannan akwai wasu lambobin da suke tsakanin masu jan rubutu da masu koren rubutu, 

Sannan daga samansu an rubuta PRICE da AMOUNT , Amount yana nufin adadin coin ko token da wani ya saka limit order zai siya ko ya siyar, Price yana nufin farashin da yake so ya siya ko ya siyar da wannan coin ko token din da ya saka a limit order,

Masu koren rubutu suna nufin wasu ne suka saka Buy Limit Order, ma’ana a siya musu wannan coin ko token din idan ya sauko daga farashin kasuwa zuwa ga farashin da suka saka a qasan Price, 

Masu jan rubutu suna nufin wasu ne suka saka Sell Limit Order ma’ana a siyar musu da wannan coin ko token din yayin da ya tashi sama da farashin kasuwa yakai farashin da suka saka a qasan price, 

Wanda suke tsakaninsu kuma shine ainishin farashin kasuwa wato Market Price,

Amma kuma wannan farashin kasuwar a mafi yawan lokaci bai sayuwa, wannan dalilin ne ma ya sa shafin www.nasara.com.ng yin wannan rubutu mai taken Yadda zakayi siyayya kamar a market price cikin kasuwar HOTBIT, 

To anan idan siyan coin ko token zakayi, sai ka duba wajen masu jan rubutu ka ga wanne farashi ne ya maka, idan ka ga farashin da ya maka sai ka ta6ashi za ka ga ya fito a gefen hagu qasa da wajen da aka rubuta Buy Sell, sai ka daidaita na yawan kudin da kake so ka siya, kamar yadda ka saba siyayya sai ka danna BUY nan take za a siya maka kamar a market price, 

Idan kuma siyarwa zakayi sai ka duba wajen masu koren rubutu ka za6i farashin da yayi maka sai ka dannashi za ka ga ya fito a gefen hagu qasa da waje da aka rubuta Buy Sell, sai ka daidaita na yawan kudin da kake so ka siyar sai ka danna SELL, nan take za a siyar maka kamar a market price, 

SHIGA NAN Ka Karanta Yadda Za Ka Mayar Da USDT Zuwa nUSD 

Ka Lura Da Wadannan Abubuwan:-

  • Sai dai duk da haka wani lokacin ana yin dace ka siya ko ka siyar a farashin da yake kasuwa  wato market price a wannan lokacin ba tare da ka ta6a Limit Order ta wani ba, saboda sai ka fara gwadawa da market price. 
  • Sannan yana da kyau ka sani matuqar siya za kayi idan har kana so ka siya nan take dole ne ka ta6a Order da aka saka za a siyar wadda farashinta ya haura farashin kasuwa, balle ma ba za ka ta6a ganin Sell Limit Order qasa da farashin kasuwa. 
  • Idan kuma siyarwa kake so kayi nan take shima dole ka ta6a Order wadda take farashinta yayi qasa da farashin kasuwa, haka nan ma ba za ka ta6a ganin Buy Limit Order sama da farashin kasuwa ba.
  • Sannan dole ka lura da Order da za ka ta6a ka tabbata yawan coin ko token din da za ka siya yayi daidai da yawan token ko coin din da yake kan Order da ka ta6a, ko kuma yafi yawan token din da kake son siya.
  • Haka idan siyarwa zakayi dole Order din da za ka ta6a yawan coin ko token da yake kanta yayi daidai ko yafi yawan token din da kake son siyarwa. 
  • Amma ka na iya siya ko siyarwa da kadan-kadan ta hanyar ta6a Order da take da token qasa da yawan wanda kake so ka siya ko ka siyar.
  • Wannan itace hanya mafi sauqi da shafin www.nasara.com.ng ya binciko wadda zaka iya siye da siyarwa a kasuwar HOTBIT nan take kamar a market price ba tare da 6ata lokaci ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button