Yadda Za Ka Zama P2P-BOSS Kafi Qarfin A Damfareka Ko A Zalunceka Ko A Cuceka A P2P
Yadda Za Ka Zama P2P BOSS Kafi Qarfin A Damfareka Ko A Zalunceka Ko A Cuceka A P2P
PEER TO PEER (P2P) Hanya ce ta zamani da ake amfani da ita wajen tura kudade ko wasu abubuwa masu muhimmanci daga wani waje zuwa wani waje ba tare da anyi hulda da hukumomi ba.
Kamar yadda mu ka sani a kasuwancin Crypto ana amfani da Hanyar P2P wajen saka kudi a cikin kasuwannin cinikayyar kudaden Crypto Currency ta hanyar amfani da wakilai wanda sukayi rijista da kasuwannin Crypto Currency a matsayin Merchant.
MERCHANT shine wanda ake sayan USDT a wajensa ko kuma a sayar masa a P2P.
Daman can akwai tsarin P2P wanda ake amfani da shi a wasu al’amura na yau da kullum wanda suke da alaqa da kasuwanci.
Kafin fara amfani da P2P anan Nigeria masu kasuwancin Crypto Currency suna iya tura kudi zuwa asusunsu na kasuwannin Crypto Currency wato “Wallet” daga bankinsu ba tare da amfani da fasahar P2P ba.
Amma saboda haramcin da babban bankin Nigeria wato CBN ya saka na hana bankuna mu’amala da kudaden Crypto Currency dole aka kar6i fasahar P2P domin isar da kudade zuwa asusun kasuwannin Crypto Currency.
Duk da haka a yanzu ana amfani da wasu katika wato ATM Cards wajen saka kudi a kasuwannin Crypto Currency.
Amma dai fasahar P2P itace hanya mafi kar6uwa a wajen masu wannan kasuwanci kuma mafi shahara.
Sai dai wannan fasaha ta P2P da ake amfani da ita a wasu kasuwannin Crypto Currency kamar BINANCE, KUCOIN da OKEX ana samun matsaloli na damfara ko zalunci a cikinta wanda hakan yana tadawa da yawa daga cikin masu wannan kasuwancin na Crypto Currency hankali, yayin da zasuyi P2P nutsuwarsu tana gushewa har sai sunga kudinsu sun dira cikin asusunsu sannan nutsuwa take dawo musu.
Yau shafin www.nasara.com.ng InshaAllah zai bada magani sadidan game da matsalolin da ake samu yayin P2P,
Matuqar ka sha wannan magani to InshaAllahu kafin qarfin duk wani mugu azzalumi macuci dan damfara da yake cikin fasahar P2P,
Ina nufin matuqar ka bibiyi wannan rubutun har qarshe cikin nutsuwa to daga yau sunanka P2P BOSS.
Haka idan kayi sakaci da wannan maganin wato wannan rubutun da shafin www.nasara.com.ng ya bada kyauta ruwan Allah to ina mai tausaya maka akwai qura wadda wannan rubutun na shafin www.nasara.com.ng kadai zai iya kade maka ita.
Biyomu a sannu domin shan wannan magani……
HANYOYIN DA ZA KA BI DON ZAMA P2P BOSS
- BADGE
- VOLUME OF TRADE
- PERCENTAGE OF TRADE COMPLETED
- HIGH/LOW PRICE
1. BADGE:- Wannan wata alama ce da ma’anarta a hausa shine bajo, mun san bajo da ake manna mana a jikin aljihunnan kayan makaratarmu wanda yake nuna tambari da sunan makaratar da muke, to haka a P2P a Binance suna bada wannan bajo ga Merchant din da ya cika wasu qa’idoji na musamman, wanda hakan yake nufin ba kowa bane yake da wannan bajo ba.
Duk Merchant da ka gani da wannan bajo a P2P to da gaske yake kasuwanci yake na saye da sayarwa, da wuya ka ga mai wannan badge din ya cuceka ko ya zalinceka ko ya damfareka,
Saboda haka duk lokacin da zakayi P2P ka yi qoqari ka nemi wanda yake da wannan Badge din,
Yadda zaka gane Badge:- Idan ka duba a qarshen sunan Merchant za ka ga wata alama ta “TICK ☑” za ka ganta da “yellow Color”, wannan ita ake kira da Bajo a hausa wato “Badge” da turanci kenan. Duba hoton da ke qasa gashinan an nuna shi da koriyar kibiya (Blue Arrow).
2. Number Of Trades:- Abu na biyu da za ka duba domin zama P2P Boss shine adadin cinikayyar saye da sayarwa da Merchant Yayi wato “Number Of Trades”, Ka tabbata duk Merchant din da za ka sayi USDT a wajensa ko za ka sayar masa yawan Trades dinsa ya kasance yana da yawa kamar daga 500 zuwa sama, akwai wanda suke da trades guda 1k, wasu 2k wasu sama da haka, domin ka zama P2P Boss ka tabbata ka duba wanda Trades dinsa ya kai daga 500 zuwa sama, kuma ina qara baka shawara idan da-so-samune ka duba wanda trades dinsa ya haura 1k, ina mai tabbatar maka InshaAllah kafi qarfin damafara ko zalunta, domin duk wanda ka gani da yawan trades 1k zuwa sama hakan yana nufin yayi cinikayyar da yawanta ya kai wannan adadin Trades din, Ka ga wanda ka gani da Trades mai yawa da gaske yake ba wasa ko batun damfara, Domin ganin yadda za ka gane yawan trade na Merchant duba hoto da ke qasa gashinan an nuna shi da farar kibiya (white arrow).
3. Percentage Of Trade Completed:- Wato Kaso nawa ne na Trade ya gama successfully, Bayan ka duba yawan Trades to har yanzu shafin www.nasara.com.ng bai gama baka takardar shaidar zama P2P Boss ba, da sauranka, abu na gaba da za ka duba shine Yawan Trades din da ya gama ba tare da anyi canceling ba,
Wani za ka ganshi da Number Of trades kusan 1k ko sama da haka amma idan ka duba Percentage of trade Completed sai kaga 70% ko 80% ko 90% ko sama da haka, wannan Percentage din da aka nuna shi yake baka labarin kaso nawa ne na yawan trades din Merchant yayi su successfully ba tare da wata matsala ba, Anan idan har ka ga Merchant da Percentage of trades Completed qasa da 90% to ina baka shawarar ka qara gaba ka nemi wanda ya kai 90% zuwa sama hakan zai fi baka damar zama P2P Boss, amma wanda ka ga yana da trade da yawa sama da 1k ko 2k sannan sai ka ga Percentage dinsa a wajen 80% ko 85% zuwa 90% to kana iya yin P2P da shi, amma matuqar har akwai wanda Percentage nasa ya kai 90% zuwa sama to ka tafi zuwa gareshi, Domin ganin Percentage Of Trade Completed duba hoto da ke qasa gashinan an nuna shi da jar kibiya (Red Arrow).
4. HIGH/LOW PRICE:- Farashi mai tsada ko mai sauqi shima abu ne mai muhimmanci da za ka duba duk lokacin da zakayi P2P, lokacin da za ka sayar da USDT a P2P idan har kana lura za ka ga farashin yadda wasu suke sayan USDT yafi na sauran tsada, Misali:- idan ace mafi yawancin Merchant suna sayan duk USDT 1 akan N550 to za ka ga wasu ‘yan tsiraru suna sayanta akan N600 ko wani farashi mai kama da haka, Idan saya zakayi za ka ga wasu sun saka farashi mafi sauqi, To ka kiyayi masu saka farashi mai tsada lokacin da za ka sayar haka ka kiyayi masu saka farashi mai sauqi lokacin da za ka saya, Sanin hakan da kiyayewa shi zai tabbatar da kai a matsayin cikakken P2P Boss kafi qarfin damafara.
5. Abu na gaba shine duk lokacin da za kayi P2P bayan ka kiyaye abubuwan farko da muka zano guda 4 to ka yi qoqarin neman dan uwanka musulmi kuma bahaushe, hakan zai taimaka wajen rage fargaba agareka a matsayinka na P2P Boss, hakan kuma zai taimaka wajen magance matsala da fahimtar juna cikin sauqi.
6. Duk lokacin da za kayi P2P kana kula da sunan Merchant domin ko da kun samu matsala da shi to nan gaba za ka kiyaye yin mu’amala da shi, haka idan har kuma bashi da matsala to ka ga ka samu abokin kasuwanci sai ka rinqa kasuwanci da shi har ku samu sabo da fahimtar juna.
7. Duk lokacin da zakayi P2P bayan ka shiga shafin da Merchants suke to ka tafi can qasa domin mafi yawancin Merchant wanda suke fitowa a farkon shafin P2P za ka ga sune masu qarancin Trades, kuma sune masu saka farashi mai tsada yayin da za su sayi USDT a wajenka kuma sune masu saka farashi mai sauqi yayin da za su sayar maka kuma sune sabbin Merchant wanda har yanzu ba a tabbatar ba shin kasuwanci suka zo ko damfara.
8. A matsayinka na mai son zama P2P Boss kafi qarfin tsoro da fargaba, lokacin da zakayi P2P tsoro ba naka bane, Boss aka ce fa, Haba Boss fa, tsoro ma ai tsoronsa yake, Abin da nake son nuna maka anan shine wata matsalar tana faruwa ne ta dalilin tsoro da fargaba wanda su kuma 6arayin nutsuwa da kwanciyar hankali ne, matuqar kuma babu nutsuwa da kwanciyar hankali to tabbas komai na matsala zai iya faruwa, saboda haka lokacin da zakayi P2P ka zama namiji na gasken gaske.
9. Duk lokacin da zakayi P2P bayan ka shiga cikin profile din Merchant za ka saka order kafin kayi hakan ka tabbata ka duba “Terms and Conditions” na wannan Merchant din, domin duk Merchant za ka ga suna saka wasu qa’idojinsu matuqar zakayi P2P da su sai ka cika wadannan qa’idojin ko ka bi dokokinsu, daga cikin irin qa’idojin da dokokin akwai wanda zai ce ba ya tura kudi zuwa wasu Bankuna saboda suna bashi matsala, wani zai ce zai dauki N100 a matsayin kudin transaction wani zai ce sai ka fara sakar masa USDT zai tura maka kudinka, wani zai ce ba ya san jinkiri wani zai ce duk matsalar da aka samu ba ya cancelling order, wani zai ce idan ka saka Order ka masa waya da sauransu dai, saboda haka kafin ka saka Order sai ka duba “Terms and Conditions” na wannan Merchant idan sun maka sai ka cigaba idan basu maka ba sai ka dawo ka duba wani Merchant din.
10. Duk abin da zakayi ba P2P ba ko menene ka nemi dacewa a wajen Allah SWT, Shi kadai yake da cikakken ikon baka kariya akan komai, amma kuma riqo da sababi shine silar samun kariyar, ka nemi taimakon Allah sai Allah ya taimakeka, Allah ya kare mana dukiyarmu. Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.
Wannan shine cikakken bayani akan Yadda Zaka zama P2P BOSS kafi qarfin damafara ko zalunci.
Domin neman qarin bayani sai a tuntu6emu a lambar wayarmu ta 07035791120 amma ta hanyar saqon whatsapp.