Yan Ta’adda Sun Kashe Ango Tare Da Amaryar Sa Mai Dauke Da Juna Biyu

Yan Ta’adda Sun Kashe Ango Tare Da Amaryar Sa Mai Dauke Da Juna Biyu

Assalamu alaikum barkan ku da kasance damu cikin wani sabon labarin abinda ya faru da wasu magidanta subahanallah.

 

A ranar da wannan abin zai faru Auwal ya dauki amaryarsa Rabiatu inda ya kai ta dakin haihuwa dake Kwatas din Masukwani saboda laulayin ciki da take fama da shi.

 

Zuwa bayan isha’i duk a ranar, dan uwansa Rabi’atu saiya ziyarce shi tare da matarsa Mai suna Aisha bello yarima.

Sun dade suna tattaunawa a kan rayuwa har sai da Rabi’u yace za su koma gida da matarsa.

 

Ba su dade da tafiya ba inda suka bar Auwal kwance a kan tabarma yayin da amaryarsa ke kwance kusa da shi, kawai ‘yan bindiga suka bayyana tare da zagaye gidan. Ba su yi harbi ba a kofar shiga saboda dare bai yi sosai ba.

 

“Yan ta’addan sun baiwa Auwal umarni amma yayi shiru” a lokacin da suka fusata sai suka ce zasu tafi da Auwal tare da matarsa.

 

Nan kuwa Auwal yace babu inda zasu je Ya tashi ya rufe hanyar shiga dakin amma cike da rashin sa’a suka harbe shi, a kafa nan take Auwal din ya fadi.

 

Bayan faduwar Auwal din nan take wani daga cikin yan ta’addan yayi kokarin afkawa dakin matar auren ta Auwal, domin ya dauko ta sutafi da ita wannan lokacin.

 

“Ganin haka yasa auwal Kara yunkurin kare matar sa, daga wannn mutane tuni ya kai kafar shi ta dama domin kara ceton amarya tasa, nan take suka harbi dayar ma.

 

Kafin ya ankara wani fusataccen mutum daga cikin su’ ya dirka masa bindiga akan shi, tare da karya masa kafar dama da kuma hannaye shi nan take.

 

Bayan sun dauko matar mai ciki nan take suka fara azabtar da ita da kuma abinda yake cikin cikinta, ganin haka yasa mijin nata bai hakura ba yayi kokarin cizon daya daga cikin mutanan.

 

Yayin da ganin yunkurin magidanci akan matar tasa kawai sukayi ta ragar gazar su, wannan lokaci har takai ga sun kashe Auwal din tare da matar sa.

 

“Yanzu haka dai jami’an tsaro suna kan binciken wannan lamari daya faru na wannan mutane a garin da abin ya faru.

 

Kada ku manta kuci gaba da bibiyar shafin ku mai farin jini

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button