Yanzu Yanzu Fati Niger Ta Fusata Tayi Zazzafan Martani Zuwaga Rarara Da Aisha Humaira A Cikin Wannan Bidiyon

Yanzu Yanzu Fati Niger Ta Fusata Tayi Zazzafan Martani Zuwaga Rarara Da Aisha Humaira A Cikin Wannan Bidiyon

Mata na cikin garari.

~~~~

 

Wato matan wannan zamanin suna cikin tashin hankali da jarrabawa. Wallahi a yau mun wayi gari, 8 out of 10 women are sexually harassed. Kuma baga matan aure ba baga yan mata ba. Kowace mace bata fi karfi namiji ya neme ta ba. Wai don masifa mace ce tazo da yaran mata marayu gidan mijin ta amma so yake ya lalata mata yara.

 

Haka zalika, yanzu mace bata isa taje neman aiki ba sai wani ya neme ta da iskanci. Hakanan idan harkar karatu ne, ko harkar neman promotion a wajen aiki, idan baki bada kan ki ba baza ki samu biyan bukata ba. Sai kaga mutum ya tsufa, old enough to be her grand father amma so yake yayi lalata da ita. Innalillahi wa inna ilaihi rajuun. 😭

 

Toh don Allah ta ina Allah zai mana albarka? Taya Allah zai dubi lamarin mu? Taya Allah zai kare mu daga sharri mugayen shuwagabanni?

 

Wasun mu sai suyi ta kullen matan su da yayan su. Wai kar suje a lalata su, bayan su haka suke lalata yayan wasu. To wayo zaka yi wa Allah? Ko kana ganin ba za’a shigo har gidan a lalata su ba? Wallahi kayi kadan.. 😁 Abinda kayi shi sa’a maka.

 

Gasu nan matan aure. Idan dare yayi a TikTok suke baje kolin su. Su bude jiki a basu kudi. Su fita suje hotel suyi iskanci kai kana kasuwa ko office kana tunanin suna gida. Hakkin ai ba wasa bane.

 

Yan uwa na mata Allah ya kare ku. Allah ya tsare ku. Allah ya baku hakuri. Wata baiwar Allah take ce min. Yau shekara 6 da auren ta ya mutu. A shekara 6, tayi mazan aure sama da hamsin, manya, matasa, ustazai, tsoffi, etc, duk wanda yazo kamar abin arziki, da an kwana biyu sai ya fara kai mata hannu. Har yau ta kasa aure. Tace kowa dan iska ne. Ta fasa.

 

Don Allah kuyi hak’uri akwai masu mutunci a cikin mu. Ku dai ci gaba da addua. Allah ya bamu. Sannan a ci gaba da rike mutunci. Allah zai kawo mafita.

 

Yawan zinace zinace shike kawo mana fitintinu a doran kasa. A rage don Allah. Sannan ga HIV da cututtukan zamani irin su hepatitis da STDs.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button