Yanzu Yanzu Rarara Yayi Kyautar Mota Da Naira Miliyan Daya.

Yanzu Yanzu Rarara Yayi Kyautar Mota Da Naira Miliyan Daya.

YA SAKA MATAR SA KUKA !

———————————————

Wani babban jami’in gwamnati ne, lokacin da matarsa taga dama ta samu, sai tace masa “ya kamata kayi amfani da damar da ka samu

kaima ka siya mana katafaren gida na alfahari, ko kuma ka gina mana, domin zai zama abin kunya ace babban mutum irinka, mai babban muqami yana zaune a irin wanan gidan.

 

Qananan ma’aikatan da basu Kai koda rabin ka ba suna rayuwa cikin babbar daula amma kai ka tsaya a

haka”…

 

»Lokacin da ta kai aya a zancenta sai yayi murmushi, ya ce: “To zan duba”.

»Washe-gari sai ya ce mata ta shirya zasu fita bayan gari.

 

Gida, ya ke so ya siya, ko kuma filin

da zaiyi mana gini zai nuna min ‘oho!! Haka ta dinga faɗi, ita kaɗai a ɗaki lokacin da take shiryawa.

 

>BASU TSAYA A KO INA BA SAI MAQABARTA! Ko marfin mota ta kasa buɗewa domin ta fito, sai

shi (mijin) Yasa hannu ya buɗe yace ta fito.

Bayan ta fito yace mata ta kalli gaba ɗaya maqabarta nan, sannan ya ce mata: –

 

Shin, yanzun zaki iya banbance min waɗanda suka ji daɗi da holewa da kuma waɗanda suka tsaya a kan

gaskiya?? Tace “a’a”.

 

Shin yanzu waɗanda suka ji daɗin a baya, ta hanyar zalunci, ko jin daɗin duniyar bai qare bane ?? Tace “ya qare”.

 

Shin, yanzu akwai wanda zai iya fitowa ya nemi yafiyar jama’ar da ya cuta bisa zalunci a cikinsu ?? Tace “a’a”.

 

Shin, kin taɓa ganin wani ya mutu sannan ya tashi ya ware da gudu yace shi bazai zo maqabarta ba??

Tace “a’a”.

 

Daga nan sai ya dubeta ido-da-ido yace “to wanda karshen gidansa wannan ɗan tsukukun wajen ne, don me zai Zalunci mutane ya kwashe

kudinsu don ya gina kantameman gida don Allah, indai yana da hankali da tunani?? Bayan yasan Akwai Hisabi…

 

Dan haka ina mai baki shawara da ki taimaka min da shawarar da zamu tsira a gaban Allah, ba wadda idanuwan mu zasu raina fata ba. Ni da ke a cikin wannan dan ramin.

 

DAGA NAN SAI TA FASHE DA KUKA TACE TA GODE WA ALLAH DA YA BATA MIJI MAI TSORAN ALLAH.

 

Yaa Allah ka bamu mata nagari da zuri’ah ɗayyiba, Allah Ka sa mudace da Arziki ta hanyar halal.

 

Daga shafin: Abubakar Sadiq.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button