Yanzu Yanzu sabuwar rigima ta barke a tsakanin yan Kwankwasiyya da yan gandujiya

Yanzu Yanzu sabuwar rigima ta barke a tsakanin yan Kwankwasiyya da yan gandujiya

Wasu Dattawan Jahar Kano Sun Yi Kira Ga Malam Ibrahim Shekarau Da Ya Haɗa Kai Da Gwamna Ganduje Da Muhimman Mutane Domin Tabbatar Da Nasarar Gawuna A Zaben Ranar Asabar Mai Zuwa

 

Haɗakar wasu dattawan Jihar Kano masu fafutukar samarwa Jihar Kano kykkyawar makoma, sun yi kira ga tsohon gwamnan Jahar Kano, Sardaunan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da ya haɗa kai da mai girma gwamnan Jahar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin ganin Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya samu nasarar lashe zaɓe ya zama gwamnan Kano.

 

Dattawan waɗanda su ka tattauna da manema labarai a safiyar wannan rana su ka kuma nemi a sakaya sunansu, sun ƙara da yin kira ga Malam Ibrahim Shekarau da gwamna Ganduje da su taru su jawo ƙarin sauran muhimman ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki da duk wani wanda zai iya ba da gudunmawa wajen tabbatar da wannan nasara ta fatan ganin Gawuna ya zama gwamna 2023.

 

“Gwamna Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau Giwayen ƴan siyasa ne a Jihar Kano waɗanda haɗuwarsu waje ɗaya zai ba da gagarumar nasara.

 

Ganduje gwamna ne mai ci a yanzu ya na da tasiri matuƙa, Malam Ibrahim Shekarau tsohon gwamna ne, kuma har yau ya na da ɗumbin mabiya waɗanda duk abin da ya ce musu za su yi biyayya.

 

Sannan kuma duk ɗinsu sun taɓa tsayawa zaɓe sun san makamar cin zaɓe, dan haka mu na ganin idan su ka haɗa kai su ka kuma janyo ƙarin gogaggun ƴan siyasa da masana daga ɓangarori daban-daban to ba shakka Dr. Gawuna ya ci zaɓe an gama da yardar Allah”.

 

Haka zalika, “Mun san Dr. Gawuna ciki da bai, a halin da Jahar Kano ke ciki yanzu, babu wani mutum da ya dace ya zama gwamna sama da Gawuna. Ya na da tsare-tsare na gina matasa da raya birni da karkara.

 

Akwai ɓoyayyun ajandodinsa kan gina goben matasa waɗanda shi ma da kansa bai bayyana ba har zuwa yau, amma mu mun san da su. Ajandodin kuwa sun haɗa da jawo matasa masu basira da ƙwarewa a fannoni daban-daban na kasuwanci, sana’a ayyuka, da dabarun dogaro da kai domin yin tafiya tare da su da ba su damar bunƙasa harkokinsu da raya Kano. Ya na da ajandar ɗaukar nauyin matasa su je ƙasashen duniya su yi karatu su samu ƙwarewa a fannoni daban-daban su dawo su amfani kansu da Jahar Kano da al’ummarta”.

 

Daga nan sun ƙara da cewa Gawuna idan ya zama gwamnan Kano al’umma za su ji daɗi gabaɗaya. Domin mutum ne salihi wanda ba ya gaba da kowa, ba shi da abokin faɗa. Mutum ne mai gaskiya da tattalin dukiyar al’umma,

 

“Gawuna ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukuma, kwamishina, mataimakin gwamna, amma har yau ba a taɓa kama shi da wani laifi na fada ko rashin girmama manyan gari ko malamai ba ba, tabbas idan ya zama gwamna zai tattala dukiyar Jaha ya shimfiɗa ayyuka a birni da ƙauyuka ya kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jihar, mu na fatan al’umma su ba shi wannan dama”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button