Yanzu Yanzu Shugaba Buhari Ya Bada Umarnin Abude Makarantun Jamio’i Kowani Dalibi Ya Koma Makaranta

 Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da jami’o’i (NUC) ta umarci shugabannin jami’a da su gaggauta bude makarantu kana dalibai su koma karatu.

Wannan na fitowa ne daga wata wasikar da ke dauke da sa hannun daraktan kudi na NUC, Sam Onazi a madadin babban sakataren hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed.

Jairdar Punch ta ce ta samu wasikar ne kai tsaye daga hukumar, inda aka umarci shuganannin jami’o’i da masu gudanar dasu da su koma bakin aiki.

Wasikar ta ce:

“Ku tabbata mambobin ASUU sun koma bakin aiki nan take; a koma harkokin yau da kullum da ayyukan jami’a na yau da kullum a dukkan jami’o’i.”

Yadda batun yajin ASUU yake

Idan baku manta ba, kotun masana’antu ta kasa a ranar Labarar da ta gabata ta umarci mambobin ASUU da su gaggauta janye yajin aiki, lamarin da ya jawo cece-kuce a Najeriya.

ASUU ta fara yajin aiki ne tun ranar 14 ga watan Satumba bisa rashin samun abubuwan da take bukata daga hannun gwamnati, haka nan Punch ta ruwaito.

An sha ganawa tsakanin ASUU da jami’ai da hukumomin gwamnati, amma lamarin ya ki kai wa ga mafita mai dorewa.

Bayan gaza shawo kan ASUU ne gwamnatin Najeriya ta maka kungiyar kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button