‘Yar Shekara 57 Da Ta Ke Da Burin Zama Malamar Jinya Ta Koma Karamar Sakandare Domin Cikar Burinta (Gemu Bai Hana Ilimi)
‘Yar Shekara 57 Da Ta Ke Da Burin Zama Malamar Jinya Ta Koma Karamar Sakandare Domin Cikar Burinta
Elizabeth Yamoah mai shekaru 57, wata ‘yar kasar Ghana da ta koma karamar sakandare domin ci gaba da karatu Domin Cika burinta na zama malamar jinya wato Nurse a turance,
Matar wacce a yanzu haka tana da jikoki da ‘ya’ya, ta yi rajista a wata makaranta da ake kira da Agona Odoben Presby JHS, Wannan makarantar anan ne jikar wannan mata ta ke karatu wanda hakan yana nufin tare da jikanyarta za suna tafiya makaranta, tana iya yiwuwa ma ajinsu đaya da jikarta ta,
Wannan mata mai shekaru 57 ta cigaba da karatu ne da nufin cimma burinta da ganin mafarkinta na zama ma’aikaciyar jinya ya zama gaske.
Wannan jajircewa da ta yi ya zaburar kuma ya birge da yawa cikin tsaffi masu shekaru irin nata da ma wanda su ka fi ta a shekaru a fadin Afirka da ma suran qasashen da ba na Africa ba.
Da take ba da labarin ta a shafukan sada zumunta, Nana Akua Asidedua ta bayyana cewa, akwai tsofaffi da yawa da har yanzu suke son komawa makaranta amma ba za su iya yin hakan ba saboda matsalolin gida da kudi. Ta yaba wa Elizabeth don ta zama abin koyi a gare su.
An bayar da rahoton cewa Elizabeth ta yi Jarabawar Takaddar Ilimi ta Basic Education Certificate (BECE).